Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Goma Sun Mutu Cikin Wasu Fashe-Fashe A Arewacin Najeriya


Fashewar boma-bomai a Najeriya

Wasu jerin fashe-fashen boma-bomai sun girgiza wata kasuwar sojoji a arewacin Najeriya

Jerin fashe-fashen boma-bomai da su ka wakana da yammacin jiya lahadi a wani wurin cin abinci mai cunkoson jama'a a wani barikin sojojin arewacin Najeriya sun halaka mutane goma a kalla, wasu kuma fiye da ishirin sun ji ciwo.

Kwamishinan 'yan sanda na jahar Bauchi, Mohammed Abdulkadir Indabawa, ya ce fashe-fashen sun faru ne a kasuwar barikin sojoji mai cunkoson jama'a.

A wani al'amari na daban kuma da ya wakana a Zuba da ke bayan garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, an samu wata 'yar karamar fashewa a wata mashayar giya, amma babu labarin cewa an samu wadanda su ka yi tsananin rauni.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin fasa boma-boman.

Tashin hankalin nan ya faru ne jim kadan bayan shugaba Goodluck Jonathan ya yi rantsuwar kama aiki da safiyar lahadi.

A cikin jawabin shi na kama aiki, sabon shugaban kasar ta Najeriya, ya yi alkawarin yakar cin hanci da kyautata ilimi da bullo da kafofin samar da aikin yi a Najeriya, da kuma fafutukar kafa demokradiya a duk fadin nahiyar Afirka. Ya ce shi wakili ne na duka 'yan Najeriya da kuma gurorin da su ka sa a gaba.

Haka kuma shugaba Jonathan ya ce ya na shirin kawo sauye-sauye a fannin man fetur din kasar da kuma karfafa shirin yin ahuwa ga tsoffin 'yan tawayen yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

A bara Mr.Jonathan ya kama mulkin kasar Najeriya bayan rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yaradua. A watan afrilun da ya gabata aka zabe shi a matsayin sabon shugaban kasar wanda 'yan hamayya su ka ce an tafka magudi.

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar Muhammadu Buhari ya na kalubalantar sakamakon zaben a kotun, ya na mai cewa an yi magudi da na'urorin hukumar zabe aka rage mi shi yawan kuri'un shi da ya samu a arewacin kasar sannan aka karawa Mr.Jonathan yawan na shi a kudancin kasar.

Amma akasarin 'yan kallon zabe na ciki da wajen Najeriya, sun ce zabubbukan na bana, daga na shugaban kasa da na gwamnoni zuwa na 'yan majalisun dokoki, su ne mafiya gaskiya da adalcin da aka taba gani a Najeriya.

XS
SM
MD
LG