Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Ake Zargi Da Kai Hare-haren Bam a Amurka Ya Mutu


Austin Texas.

Mutumin da ake zargi da kai hare-haren bam a garin Austin dake jihar Texas ta Amurka, ya mutu ta hanyar tayar da bam a dai-dai lokacin da 'yan sanda suka tunkareshi.

'Yan sandan garin Austin a jahar Texas ta nan Amurka sun ce mutumin da ake zargi da kai hare-haren bama-bamai a garin na Austin ya mutu bayan da ya saki bom a cikin motarsa yayin da ya ga yan sanda suna tunkarar sa.

Shugaban yan sandan garin Austin, Brian Manley ya fadawa manema labarai cewa Hukumar yan sandan tana da yakinin ainihin kamannin wanda ya saki bomb din wanda suka ce wani matashin namiji ne farar fata dan shekara 24, an ga motar shi a wani otal kusa da garin Austin ranar Talata da daddare zuwa safiyar Laraba kafin ya je ya tada bom din.

Madugun ‘yan sandar ya tabattar da cewa sun yi yakinin matashin ne ke ta tayar da bama-bamai a garin Austin din tun daga ranar biyu ga watan nan na Maris, wanda har mutane biyu suka rasa rayukansu a ciki, wasu hudu suka sami raunuka.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG