Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Ya Fara Gano Gawarwakin Sojojin Amurka Da Aka Kashe a Nijar


Sojojin Amurka na musamman da na Nijar

Wani dan Nijar da yace shine ya gano gawarwakin sojojin Amurka hudu da aka kashe a watan da ya gabata, ya ce ya samesu ne cikin jini an kuma cire musu kakinsu na soja.

Adamou Boubacar, ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa, shine mutumin da ya fara ganin gawarwakin bayan da aka yi musayar wuta ranar 4 ga watan Agusta, tsakanin dakarun Amurka na musamman da ‘yan ta’addar da suka kai musu harin kwantan bauna a kauyen Tongo Tongo dake yammacin kasar NIjar.

Boubacar, dake shima mazaunin kauyen Tongo Tongo ne, ya ce lokacin da ya gano gawarwakin yana neman matarsa da ‘ya ‘yan sa ne a kusa da gurin.

Ya kuma ce ya samu sojoji biyu a cikin mota na ukun kuma kwance a ‘kasa.

Da aka tambayi Boubacar ko sojojin na sanye da kayan sarki lokacin da ya gansu, ya ce ‘daya babu kaya jikinsa, sauran biyun kuma suna sanye ne kawai da gajeran wando. An kuma dauke duk makamansu da kayayyakin aikinsu.

A jiya Juma’a Muryar Amurka ta tambayi ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, domin ta tabbatar da labarin, amma sai mai magana da yawun ma’aikatar yace yanzu haka ana gudanar da bincike, ba zasu iya magana akai ba har sa an gano abin da ya faru.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG