Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Aisha Alhassan Babban Rashi Ne – Buhari


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalanta, abokanai, Majalisar Dokoki Najeriya da gwamnati da al’umar jihar Taraba.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna alhininsa dangane da rasuwar tsohuwar ministar mata Aisha Jummai Alhassan.

Alhassan ta rasu ne a birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Jumma’a.

Marigayiyar wacce ake yi wa lakabi da “Mama Taraba” ta yi minista a gwamnatin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2018.

“Shugaban Najeriya ya shiga yanayi na alhini bisa rasuwar Hajiya Aisha Jummai Alhassan, “Mama Taraba,” wacce ta rike mukamin ministar mata a wa’adinsa na farko.” Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin Buhari Garba Shehu ta ce.

Karin bayani akan: Boko Haram, Chibok, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Rasuwar wannan fitacciyar ‘yar siyasa, Aisha Jummai Alhassan, ya bar mutane da dama cikin yanayi na alhini. A lokacin tana rike da mukaminta da kuma bayan ta kammala, babban abin da ya fi damunta shi ne, ilimin ‘ya’ya mata, musamman na ‘yan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram ta sace.”

Sanarwar ta kara da cewa, “wannan rasuwar babban rashi ne ba ga mata masu fafutuka kadai ba, har ma da kasar baki daya.”

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalanta, abokanai, majalisar dokoki Najeriya da gwamnati da al’umar jihar Taraba.”

A shekarar 2015, bayan da ta fadi zabe a jihar Taraba inda ta nemi mukamin Gwamna karkashin tutar jam’iyyar APC, Buhari ya nada ta a matsayin minister mata.

XS
SM
MD
LG