Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Muka Ziyarci Abba Kyari Ba – Zulum, Shettima


Gwamna Zulum, haru da tsohon gwamna Shettima, dama (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum, haru da tsohon gwamna Shettima, dama (Facebook/Gwamnatin Borno)

“Shi da kansa Kyari ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga watan Yuni, jim kadan bayan ziyarar.”

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da tsohon gwamna Kashim Shettima, sun musanta kai ziyara gidan Abba Kyari kamar yadda wasu rahotanni suke nunawa.

Mai magana da yawun gwamna Zulum Malam Isa Gasau ne ya fitar da wata sanarwa a ranar Laraba inda ya ce ya zama dole ya fito ya yi Karin haske kan wani bidiyo wanda ke nuna alamar Zulum da Shettima sun kai wa Kyari ziyara.

Wani bidiyo da Kyari ya wallafa a shafin sada zumunta ya nuna shi tare da gwamna Zulum da tsohon gwamna Shettima a wani falo.

“Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da tsohon gwamna, Sanata Kashim Shettima, ba su ma san gidan DCP Abba Kyari ba, ballantana har su kai masa ziyara.” In ji Gusau.

A cewar Gusau, bidiyon da ake ta yawo da shi, wasu makusantan Kyari ne suka dauka a lokacin da shi Kyari ya kai wa Sanata Kashim Shettima ziyara a gidansa da ke Abuja a ranar 30 ga watan Yuni, 2021, inda ya je yi masa jaje kan jita-jitar da ake ta yadawa cewa ya rasu a kasar Burtaniya.

“Shi da kansa Kyari ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga watan Yuni, jim kadan bayan ziyarar.”

Gwamna Zulum, haru da Abba Kyari, dama - daga dikin bidiyon da Kyari ya wallafa (Instagram/ Abba Kyari)
Gwamna Zulum, haru da Abba Kyari, dama - daga dikin bidiyon da Kyari ya wallafa (Instagram/ Abba Kyari)

Kakakin gwamnan ya ce ya zama dole ya fito ya yi karin haske kan bidiyon, saboda a cewarsa, “Kyari wanda ya yi alkawarin zai fitar da sanarwar karin haske, bai yi hakan ba sama da sa’a hudu bayan da ya yi alkawarin zai yi hakan.”

“Kyari wanda dan jihar Borno ne kuma daga mazabar Shettima, ya kai wa tsohon gwamnan ziyara ne don ya yi masa fatan samun sauki, kamar yadda wasu mutane da dama suka yi.”

Kakakin na Zulum ya yi kira ga Kyari da ya fito ya yi karin haske kan bidiyon kamar yadda ya yi alkawari.

Kokarin jin ta bakin Kyari ya ci tura, amma binciken da Muryar Amurka ta yi ya gano cewa Kyari ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram a ranar 30 ga watan Yunin 2021.

Ana zargin Kyari da karbar cin hanci daga Ramon Abbas da ke fuskantar shari’a a wata kotun Amurka bisa laifukan da suka shafi damfara ta yanar gizo da halalta kudaden haram. Kuma tuni har ya amsa aikata laifukan a makon da ya gabata.

Binciken da kotun ta gudanar ya nuna Kyari ya karbi cin hanci a hannun Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi a wata badakala ta dala miliyan 1.1.

Hakan ya sa kotun Amurka ta umarci hukumar hukunta manyan laifuka ta FBI ta kamo Kyari, wanda tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne a Najeriya.

Shi dai Kyari ya musanta zargin da ake masa, inda ya ce bai taba karbar ko sisi a hannun Hushpuppi ba.

A farkon makon nan hukumomin Najeriya suka dakatar da shi daga aiki, a wani mataki na gudanar da bincike kan wannan zargi.

Tuni har an maye mukaminsa da DCP Tunji Disu.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG