Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Iya Koyi da Soke Zaben Kenya


Mr. David Dimas
Mr. David Dimas

Wani marubuci kuma mai fashin baki kan harkokin kasashen duniya, David Dimas ya bayyana cewa Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika zasu iya yin koyi da kasar Kenya

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Mr. Dimas wanda yake da zama a Amurka ya bayyana cewa, soke zaben shugaban kasa da kotun kolin kasar Kenya tayi , da kuma bada umarnin sake sabon zabe wani lamari ne da ya kamata a yi nazari a kai kasancewa wannan ya zama wani abinda ba a saba gani ba a kasashen Afrika.

BIsa ga cewarshi, soke zaben babbar nasara ce ga starin demokaradiya, kasancewa ya nuna cewa, kotunan suna aiki., da ya zama abin alfahari. Ya kuma ce wannan ya zama babban darasi ga sauran kasashen nahiyar idan ana so a sami ci gaba da zaman lafiya.

Mr. Dimas ya bayyana aniyar shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta na sake fasalin kotun koli a matsayin mugun nufi da kuma koma baya, idan aka yi la’akari da irin asarar rayukan da aka yi sakamakon rashin gamsuwa da zabukan baya, ya kuma ce babbar jam’iyar hamayyar tana da hujja a kiran da tayi na neman a sauke jami’an hukumar zaben , a kuma sami wadansu dabam su gudanar da sabon zabe kasancewa soke zaben manuniya ce cewa, sun tafka kurakurai, abinda zai zama da wuya duk wani zabe da zasu gudaar nan gaba ya zama da karbuwa.

Ga cikakkiyar hirarsu da Sarfilu Hashim Gumel

Hira da David Dimas Kan Soke Zaben Kenya-6:40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:40 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG