Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: A Kalla Mutane Miliyan 200 Zasu Samu Lambar Zama Dan Kasa


NIMC
NIMC

Gwamnatin Najeriya tace Zata rarraba lambar zama dan kasa kimanin milyan dari biyu ga yan kasar.

A hirar su da wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, Janar Manaja mai kula da sadarwa na hukumar Abdulhamid Umar Umaisha ya kara haske akai, yace wannan mataki na da alaka da matsalar tsaro.

Wannan mataki dai na zuwa ne daidai lokacin da Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ta jaddada bukatar mallakar katin zama dan kasa a shiyyar Arewa Maso Gabas.

Hukumar NIMCI tace bada lambar zai taimaka wajen inganta matsalar tsaro, kuma hakan zai taimaka wajen tantance yan kasa, da na bakin haure. Hukumar ta nuna rashin Jin dadinta da yadda, hatta wasu yan kasashen waje kanbi haramtacciyar hanya wajen mallakar katin.

Galibin 'yan Najeriya dai basu sami lambar zama dan kasa ba, al'amari da hukumar NIMCI tace bai rasa nasaba da irin dimbin matsalolin da take fama dasu. Dalilin da yasa ake shirye shiryen shigo da karin wasu hukumomin gwamnati wajen bayar da lambar ga Jama'a.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG