An kaddamar da allurar rigakafin cutar da ake kira "Zoonoti" a Adamawa.
Manufar wannan allurar riga-kafin ita ce a yi yaki da wannan muguwar cutar da ke kama huhun dabbobi wato "Neglected Zoonotic Disease", wace yanzu ke yaduwa tamkar wutar daji.
Kuma kamar yadda asusun kula da abinci na Majalisar Dinkin Duniya FAO, da hukumar kiwon lafiya ta duniyan WHO, ke gargadi, wannan annobar cutar na iya yaduwa zuwa bani adama, ta sanadiyyar cudanya da dabbobi.
Yayin kaddamar da allurar rigakafin a yankin masarautar Ganye da ke da albarkatun noma da dabbobi a jihar Adamawa Arewa maso Gabashin Najeriya, Dr. Bartholomew Nyalas, na ma’aikatar kula da dabbobi a jihar, ya bayyana illar da cutar ke da ita ga dabbobi, da kuma dan adam.
Kwayar cutar na da illa matuka ba wai kawai ga shanu ko dabbobi ba, har ma ga dan Adam, yakan kama huhu kuma nan take ya kan kashe dabba, ga saurin yaduwa.
Hukumomin abinci, da na kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya wato FAO,da WHO, duk sun sanya cutar a matsayin annoba.
Don haka wannan riga-kafin zai taimaka, ba a wannan yanki na Toungo kadai ba, har zuwa Mayo-Belwa saboda akwai cudanya yanzu a tsakanin makiyaya da ke shigowa tun daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zuwa Najeriya, a cewar likitan dabbobin Dr. Bartholomew Nyalas.
Da yake jawabi yayin kaddamar da riga-kafin a mazabarsa, Hon. Abdur Razaq Namdas dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Toungo, Ganye, Jada da kuma Mayo-Belwa, ya ce, daukan matakin riga-kafin ya zama dole don ceto rayukan dabbobi, da kuma na al’umma, tun da a kullum akan yanka dabban dabbobi a Najeriya.
Wannan ma ko na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce game da shirin tsugunar da makiyaya a waje guda na Ruga, ko kuma Ranches, batun da dan majalisar wakilan Abdur Razaq Namdas, ke cewa idan ana kula da makiyaya to ba za’a samu matsala ba.
Ana dai sa ran yi wa shanu 100,000 riga-kafi a karon farko.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 08, 2021
Ranar Mata Ta Duniya: Mata A Jihar Borno Na Neman Dauki
-
Maris 08, 2021
Mata Suna Neman Gwamanati Ta Dama Da Su
-
Maris 07, 2021
Ba Bu Wanda Yake So Najeriya Ta Rabu - NOA
Facebook Forum