Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Zargi Barayin ‘Yan Siyasa Da Rage Karfin Sojan Najeriya


An zargi manya manyan jami’an tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan, da laifin cin hanci da rashawa

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, ya zargi barayin ‘yan siyasa wajen rage karfin sojan kasar a yaki da ake da mayakan kungiyar Boko Haram, amma masana al’amuran yau da kullum na ganin kasawar da sojojin Najeriya sukayi ba wai kawai daga matsalar sace kudin Najeriya bace kawai.

An zargi manya manyan jami’an tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan, da laifin cin hanci da rashawa cikin makwannin da suka wuce, cikin su harda tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki da Oluse Meto mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta PDP.

Baki ‘dayansu ana tuhumarsu ne da laifin karkatar da akalar kudin da aka ware domin sayen makamai ga sojojin Najeriya. yanzu haka dai Dasuki shine ake tuhuma kan kudade masu yawa, an dai amince fitar da kudi sama da dala biliyan 2 domin sayen makamai, amma bai amince da tuhumar da ake masa ba.

Kwashe shekaru 6 da Boko Haram su kayi a Najeriya, sun kashe kusan mutanen dubu 20, da tilastawa sama da mutanen miliyan 2 barin gidajensu a Najeriya. alokacin da Buhari yake yakin neman a zabe shi, yayi alkwarin murkushe ‘yan Boko Haram da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

XS
SM
MD
LG