Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Kamaru Zasu Hada Kai A Fannin Tsaro


Sojojin Najeriya su na lodin makamai cikin jirgin sama a Kaduna
Sojojin Najeriya su na lodin makamai cikin jirgin sama a Kaduna

Mukaddashin firayim ministan Kamaru, Ahmadou Ali, ya mika sako na musamman daga shugaba Paul Biya zuwa ga shugaba Goodluck Jonathan a Abuja

Najeriya da Kamaru sun kuduri aniyar yin aikii tare domin tabbatar da tsaro a bakin iyakarsu ta kasa da kum ata cikin ruwa.

A yau alhamis aka yi wata ganawa a tsakanin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da mukaddashin firayim ministan kasar Kamaru, Ahmadou Ali, wanda yayi tattaki zuwa Abuja dauke da wani sako na musamman daga shugaba Paul Biya.

A cikin wannan sakon, shugaba Biya na Kamaru ya gayyaci shugaban na Najeriya domin su gudanar da wani gagarumin taro na shata yadda zasu tabbatar da tsaron bakin iyakarsu ta kasa da kuma ta ruwa, da nufin inganta harkokin tsaron yankin Afirka ta Yamma.

Wannan yana zuwa a bayan da Najeriya ta ayyana kafa dokar-ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe a yankin arewa maso gabas, inda Najeriya ta yi iyaka da kasar ta Kamaru, da kuma kasashen Chadi da Nijar.

Kamaru dai ta rufe bakin iyakokinta ta kasa da Najeriya a bayan ayyana dokar-ta-bacin, domin tabbatar da cewa 'yan bindigar da ake farauta ba su tsallaka iyaka suka sulale cikin Kamaru ba.

Wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, ya tattauna da shugaban Kwamitin Harkokin Cikin Gida na Majalisar Wakilan Tarayya ta Najeriya, Alhaji Umar Bature, kan wannan hadin kan da ake shirin kullawa a tsakanin Najeriya da Kamaru.

Mukaddashin Firayim Ministan Kamaru Ahmadou Ali Ya Gana Da Shugaba Jonathan A Abuja - 3:23
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG