Accessibility links

Majalisar Zartaswa Ta Amince Da Kafa Dokar-Ta-Baci


Sojojin Najeriya a kauyen Baga, kusa da birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Jihar Borno. Mayu 13, 2013.

A zaman da ta yi na yau laraba, majalisar zartaswar Najeriya ta bayyana amincewarta da kafa dokar-ta-bacin da aka yi a Borno da Yobe da Adamawa

Majalisar zartaswar tarayya ta Najeriya ta bayyana cikakken goyon bayanta ga ayyana kafa dokar-ta-bacin da shugaba Goodluck Jonathan yayi a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa na yankin arewa maso gabashin kasar.

A cikin hirar da yayi da wakilin Sashen Hausa Umar Faruk Musa yau laraba a Abuja, jim kadan a bayan kammala taron majalisar, ministan yada labarai na Najeriya, Mr. Labaran Maku, yace majalisar ta cimma matsayar cewa wannan matakin da aka dauka shi ne ya dace a saboda yadda tsagera a wannan yanki suke yin barazana ga hadin kai da kuma ci gaba da kasancewar Najeriya a zaman kasa guda.

Mr. Maku yace za a ci gaba da kokarin neman yin sulhu ta hanyar kwamitin nan da gwamnati ta kafa, amma kuma a zahiri gwamnati ba zata kyale wasu 'yan bindiga su na cin karensu babu babbaka kawai ba.

Ga cikakken rahoton Umar Faruk Musa daga Abuja:

XS
SM
MD
LG