Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Hukumar Kwastam Ta Kama Shinkafar Roba Da Buhunan Tabar Wiwi


Shugaban Hukumar Kwastan na Ruwa Umar Yusuf
Shugaban Hukumar Kwastan na Ruwa Umar Yusuf

Bayan da hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu buhunan shinkafar roba, yanzu haka ta sake kama tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira Miliyan 250.

Shugaban kwastam Umaru Yusuf, ya tabbatar da cewa hukumar ta kama manya-manyan buhunan tabar wiwi har 43, wanda hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi suka kiyasta cewa kudinsu ya kai Naira Miliyan 250.

Buhunan tabar wiwi da hukumar Kwasta ta kama
Buhunan tabar wiwi da hukumar Kwasta ta kama

A cewar shugaban kwastam din kayan dai sun fito ne daga kasar Ghana, domin cikin wannan shekarar hukumar kwastam ta sha kama ire-iren wannan kayayyaki har sau biyar, wanda kudinsu yakai Naira Miliyan 700.

Game da shinkafar roba da akace an kama a gundumar hukumar kwastam dake Ikeja Lagos, yanzu haka dai an mika shinkafar ga hukumar NAFDAC domin tantancewa da tabbatar da gaskiyar lamarin.

Hukumar kwastam dai ta bukaci goyon bayan jama’a wajen yaki da ‘yan fasa kwauri a ko ina a fadin Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

XS
SM
MD
LG