Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Jiragen Yaki Sun Yi Luguden Wuta a Dazukan Kaduna


Wasu sojojin Saman Najeriya
Wasu sojojin Saman Najeriya

A cigaba da kokarin fatattakar 'yan ta'adda da ke kai hare hare a dazukan jahar Kaduna, wasu jiragen yakin sun yi ta aman wuta a wasu wuraren buyar 'ya ta'adda a dazukan jahar Kaduna.

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce Rundunar Kai Farmaki ta Thunder Strike ta yi ta barin wuta akan wasu sansanonin yan bindiga biyu a jihar kaduna.

Hare Haren da jiragen yakin kasar suka kaddamar a dazukan Kuduru da Kwiambana a jihar ta Kaduna sun yi sanadin kashe ‘yan ta'adda da dama a dazukan.

Kwamandan Dakarun Ruwa (Navy Commander) Abdulsalam Sani na Hedikwatar tsaron kasar ya shaida wa muryar Amurka cewa jiragen yakin, kazalika sun rugurguza sansanonin ‘yan ta'addan.

Hedikwatar tsaron Najeriyar ta ce hare haren za a ci gaba da kai wa ne har sai an kawo karshen aika aikar ‘yan bindigar a sassan jihar.

Jiragen Yakin sojojin saman Najeriya samfurin Alpha Jet ke Atisayen kayatar da manyan baki Inda suke fitar da Hayaki kore da fari da kore wato launin tutor Najeriya
Jiragen Yakin sojojin saman Najeriya samfurin Alpha Jet ke Atisayen kayatar da manyan baki Inda suke fitar da Hayaki kore da fari da kore wato launin tutor Najeriya

Kwamanda sani ya kara da cewa wannan na zuwa ne bayanda a makon jiya su ma sojojin kasa sukai wa wasu masu garkuwa da mutane kwanton bauna, inda suka halaka hudu daga cikinsu.

A bangarenta, gwambatin jihar kaduna, ta bakin kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan ta yaba da wannan ci gaba, inda shima ya tabbatar da za a ci gaba da kai hare haren.

Aruwan ya ja hankalin jama’ar jihar cewa kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta bai da alaka da addini ko kabilanci, inda yace aika aika ne kurum na ‘yan ta'adda, kuma gwamnati na aiki tukuru don yi wa tubkar hanci.

Inda ya bayyana kwarin gwiwar maido da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan bada jimawa ba.

Ga wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG