Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Bude Filin Jiragen Sama Na Kaduna


Mutane a filin jirgi a Najeriya
Mutane a filin jirgi a Najeriya

Akalla wasu karin filayen jiragen saman Najeriya biyu ne aka tabbatar sun sake budewa domin zirga-zirgar cikin gida a Najeriya a cewar Henrietta Yakubu ta FAAN.

A cikin wani rahoton jaridar The Guardian, babbar daraktar sadarwa da hulda da jama’a ta hukumar filayen jiragen saman Najeriya (FAAN), Henrietta Yakubu, ta tabbatar da wannan ci gaban.

A cewarta filin jirgin saman Kaduna ma zai kasance a sahun wadanda za’a bude a yau.

Filayen jiragen saman Margaret Ekpo da ke Calabar da filin jirgin saman Yola a jihar Adamawa sun sake budewa.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ce za ta tabbatar da bin ka’idojin kariyar lafiya da tsaro, don kauce wa rufe filayen jiragen saman da aka sake budewa kwanan nan.

Ya zuwa yanzu, filayen jiragen saman 10 daga cikin 22 sun bude ayukan sufuri na cikin gida, a cikin matsanancin yanayin rashin fasinjoji da yawan jiragen da ke aiki.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce suna fuskantar matsin lamba matuka ta sake bude tashoshin jiragen saman, haka kuma yana fama da korafe-korafe akan dalilan da ya sa wasu filayen suka riga wasu budewa.

Sirika ya ce "abin takaici, mu na rayuwa ne a cikin kasar da komai yake tattare da sarkakiya da rikitarwa."

Hakan duk na zuwa bayan da aka shafe tsawon watanni uku na hana zirga-zirga sakamakon annobar COVID-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG