Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Ci gaba Da Fuskantar Matsalar Barkewar Cutar Kwalara


A Najeriya, ana ci gaba da samun wadanda cutar kwalara ke harba a 'yan makonnin nan, mafi akasari a arewacin kasar yayin kuma da ake fama da cutar COVID-19 a gefe guda.

Dr. Bashir Lawan Muhammad, masanin cutar kuma mataimakin daraktan kula da lafiyar al'umma na cibiyar tattalin arzikin arewacin jihar Kano ya shaida wa Kamfanin dillacin labaran Reuters cewa a cikin makonni biyu da suka gabata, an sami sabbin harbuwa.

Ya ce damina na kara munin cutar, yayin da rashin tsaro a arewacin kasar, inda hukumomi ke fafatawa da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane ke kawo cikas ga ikon hukumomin su dakile cutar.

An kimanta akalla jihohi 22 daga cikin 36 na Najeriya, da kuma babban birnin tarayya Abuja ne suka kamu da cutar ta kwalara, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya, (NCDC).

Cutar, wacce gurbataccen ruwa ce ke haifarwa, na iya kisa cikin 'yan awanni idan ba a yi maganinta ba.

Akalla mutum 186 sun mutu a Kano sakamakon cutar kwalara tun daga watan Maris, in ji Muhammad. Jihar ce ke da kaso mafi yawa na mutuwar cutar kwalara cikin mutum 653 da hukumar NCDC ta bayyana sun kamu a cikin kasar baki daya. Jihohin arewacin da ke kusa da Bauchi da Jigawa su ma suna cikin wadanda suka fi fama da cutar, a cewar NCDC.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG