Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Bi Sahun Sauran Kasashe Wajen Fara Azumi Ranar Litinin


Ramadan

An umarci ‘yan Najeriya da su tashi da azumin watan Ramadan ranar Litinin.

Mai alfarma sarkin Musulmi kuma shugaban hukumar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayar da sanarwar ganin jinjirin watan azumin Ramadan na wannan shekara.

Sarkin Musulmi ya umarci al’ummar musulman Najeriya da su tashi da azumi ranar Litinin. Haka kuma ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su tuna da shugabanni da kuma yadda yanayin kasar ke ciki musamman a sha’anin tsaro a dukkan ibadu da addu’o’i a tsawon wannan wata na Ramadan.

A wannan karon dai Najeriya ta yi muwafaka da kasar Saudiyya, wacce duk da yake ta fara duban wata tun ranar Asabar, amma ta bayar da sanarwar fara azumi ranar Litinin.

Saurari sanarwar mai alfarma Sarkin Musulman Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG