Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fara Daukar Mataki Akan Wadanda Aka Ambato Su A Binciken "Pandora Papers"


CODE OF CONDUCT BUREAU UPDATE ON PANDORA PAPERS PROBE

Tuni muka fara gudanar da bincike a kan jami'an gwamnati da sunayensu ya fito a leken asirin Pandora Papers- Farfesa Mohammad Isah

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Bureau (CCB) ta bayyana irin kokarin da ta ke yi na binciken jami’an gwamnati na baya da na yanzu da ake zargi da mallakar kaddarori ba bisa ka’ida ba

Shugaban Hukumar Farfesa Mohammad Isah ya ja hankalin jama’a da ma’aikatan gwamnati a kasar zuwa ga aikin tattacen kaddaorinsu inda ya ce an fara daukan matakai a kan ‘yan kasar da binciken PANDORA PAPERS ya bankado sun mallaki kaddarori da kudadde na haramun a kasashen waje

Farfesa Mohammad Isah ya kara da cewa hukumar wacce aka dorawa nauyin tabbatar da dukkan masu rike da mukammi na gwamnati sun bayyana kadarorin da suka mallaka ta na aiki tare da mambobin kungiyoyi masu zaman kansu wadanda da su aka yi aiki bankado mutanen da ake zargi, y ace akwai saura wasu jami’an gwamnati da ake kokarin neman Karin bayani akan rawar da suka taka a binciken na Pandora Papers.

Ya kuma kara da cewa suna daukar sabbin matakai na tabbatar da masu rike da mukami na gwamnati da na siyasa sun bi kaidojin da ya kamata wajen bayyana kadarorinsu da suka mallaka kuma dole ne ko wanne ma’aikaci ya bayyana abin da ya mallaka

kungiyar CISLAC dake yaki kan ayyukan cin hanci da rashawa a Najeriya ta bakin shugabanta a Najeriya Awwal Musa Rafsanjani ta goyi bayan wannan yukuri da hukumar ta ke yi inda ta ce sai an karfafa ayyukan hukumar idan har na so a yi yaki da ayyukan cin hanci da rashawa a Najeriya

Sai dai daga cikin kalubalen da hukumar ke fuskanta karancin ma’aikata da kudin albashi na daga ciki, a cewar shugaban hukumar ta na da ma’aikata 800 a fadin kasar wadanda ke aikin tantance kaddarorin jami’an gwamnati miliyan 10 wanda hakan ba karamin tarnaki bane idan ba’a yi saurin maye gurbin wadanda suka nutu ko suka yi ritaya ba

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG