Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Hada Maganin Rigakafin Korona Guda Biyu - Boss Mustapha


Sakataran Gwamnatin Tarayyar Najeriya Mr. Boss Mustapha

Masana kimiya a Najeriya sun hada alluran rigakafi guda 2 don yaki da annobar cutar korona kamar yadda shugaban kwamitin yaki da cutar kuma sakataren gwamnatin tarrayar Najeriya Boss Mustapha ya sanar.

Boss Mustapha ya ce ana cigaba da gudanar da gwaje-gwaje a kan sabbin magungunan rigakafin kuma da zarar an kammala za'a fara amfani da alluran.

Mustapha ya kara da cewa, wannan wani gagarumin ci gaba ne da zai kara martabar bangaren kiwon lafiya a Najeriya, ya kuma yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki dsu bada goyon baya da duk gudumawar da ta dace don ganin an tabbatar da samar da rigakafin.

Da yake karin bayani game da rigakafin, jami'i a ma'aikatar lafiya ta Najeriya, Dr. Ibrahim Kana, ya ce tun a karshen shekarar 2020 wasu masana kimiyya a wasu jami’o’i a Najeriya suke ta bincike a kan korona biros wanda daga karshen shekara suka gwadawa ma’aikatar kiwon lafiya a kan cewa binciken ya nuna musu lallai tabbas sun samo ainihin rigakafin da zai iya taimakawa.

Ya kuma kara da cewa sun ce bincikensu ya nuna cewa, rigakafin yana aiki har kashi 90 cikin 100, wannan binciken dai sun yi shi ne a dakin bincike kuma kafin a fara amfani da rigakafin sai an yi gwaje gwaje a matakai daban-daban da zai kai daga mataki na daya zuwa na uku wanda wani lokacin ma har zuwa na hudu.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya ce za’a gwada rigakafin a jikin dabbobi da mutane a tabbatar yana yin aiki kafin a fara yiwa mutane gaba daya, sannan a tabbata ba su da illa a jikin mutane, amma kafin a kai ga wannan ana bukatar kudin da ya kai kimanin dalar Amurka dubu dari don kammala binciken.

A nasa bangaren kwararren likitan yara da ke aiki da shahararren asibitin kasar Turkiyya da ke Abuja wato Nizamiye Hospital, Dr. Lawal Musa Tahir, ya ce idan har za'a bi dukkan matakan da ya dace kasar zata iya hada rigakafin tare da bada misalin wasu nau'i na rigakafi da kasar ke yi.

Ya ce matukar za’a bi dokokin da ya kamata za’a iya samar da allurar rigakafin korona biros a Najeriya kuma idan aka yi hakan cigaba ne sosai wanda ya kamata a ce kasar ta fara yiwa kanta da ya dace ba wai sai sun jira wata kasar ta yi musu ba.

Idan za'a iya tunawa a rana 2 ga watan Maris na wannan shekarar ne Najeriya ta karbi kason farko na allurar rigakafin korona kimanin miliyan hudu, inda tuni aka fara yin allurar a daukacin jihohin kasar bai daya.

Sai dai kuma kiyasin yawan 'yan kasar ya kai miliyan 200 , sabili da haka, ana ganin wannan wata dama ce da samar da rigakafin da zai ishi kowa a kasar duk da cewa mutane da dama na nuna kin amincewa da allurar rigakafin.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00


Dubi ra’ayoyi

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG