Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lallasa Ethiopia Da Ci 4 Da Babu


Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles" a filin wasa na kasa dake Abuja, inda aka lallasa 'yan Ethiopia da ci 4 da babu, lahadi 27 Maris, 2011
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles" a filin wasa na kasa dake Abuja, inda aka lallasa 'yan Ethiopia da ci 4 da babu, lahadi 27 Maris, 2011

Dan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin dubban 'yan Najeriya da suka halarci wannan wasan share fagen cin kofin kasashen Afirka a Abuja

Sabon mai koyar da 'yan wasan na Najeriya, Samson Siasia, yayi fitowar sa'a a wasansa na farko (wanda ba na sada zumunci ba) a bayanda 'yan Super Eagles na Najeriya suka doke 'yan wasan Ethiopia da ci 4 da babu a wasan share fagen zuwa gasar cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka.

Peter Utaka da dan wasan da ya canje shi daga baya, Ikechukwu Uche, sune suka jefa wadannan kwallaye hudu a ragar 'yan Ethiopia a wannan karawa da aka yi jiya lahadi a filin wasa na kasa dake Abuja, babban birnin Najeriya.

Tun ma kafin cikar minti daya da fara wannan wasa, Utaka ya jefa ma Najeriya kwallon farko, sannan a cikin minti na 53 kuma ya lale mai tsaron gidan 'yan Ethiopia, Zerihun Derese, ya jefa kwallo na biyu.

A bayan da ya jefa kwallo na biyu da aka komo daga hutun rabin lokaci, sai nmai horaswa na Najeriya ya canja Utaka domin ya huta, ya shigar da Uche, wanda shi kuma ya jefa kwallo na uku a minti na 78 da fara wasa. Ana dab da tashi kuma, sai Uche ya jefa kwallo na hudu a raga, ya rufe bakin 'yan Ethiopia.

Dan wasan Najeriya, Obafemi Martins, yana gaida Muhammadu Buhari, a filin wasa na kasa dake Abuja lokacin wasan Najeriya da Ethiopia, Lahadi 27 Maris 2011
Dan wasan Najeriya, Obafemi Martins, yana gaida Muhammadu Buhari, a filin wasa na kasa dake Abuja lokacin wasan Najeriya da Ethiopia, Lahadi 27 Maris 2011

Daga cikin wadanda suka hallara a filin wasan an kasa dake Abuja domin kallon wannan kwallo, har da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC a zabe mai zuwa, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, wanda jama'a suka gani kwatsam a tsakiyar 'yan kallo. Mutane da dama sun je sun gaida shi cikinsu har da wasu 'yan wasan na Najeriya bayan da suka gano cewa shi ne.

Wannan nasara da Najeriya ta samu dai ya fara kwantar da hankulan wasu 'yan kallo na Najeriya wadanda a baya suka damu da irin rawar da kungiyar zata taka, kuma ko zata kai labari.

mai koyar da 'yan wasan Super Eagles, Samson Siasia, ya ce wannan mafari ne mai kyau, kuma zasu yi kokarin taka rawar gani sosai.

Mai koyar da 'yan wasan Ethiopia, wanda asalin dan najeriya ne, Iffy Onuora, yace Najeriya tana da kwararrun 'yan wasa dake bugawa a manyan kulob-kulob na duniya. Yace 'yan wasansa ba su da kwarewa kamar ta 'yan Najeriya, kuma an ga hakan a filin wasan.

XS
SM
MD
LG