Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uche Okechukwu Ya Jefa Kwallonsa Na Farko, Ya Kuma Barke Da Kuka


Uche Okechukwu bayan da ya jefa wani kwallo ma Najeriya lokacin gasar cin kofin duniyar da ta shige a Afirka ta Kudu.
Uche Okechukwu bayan da ya jefa wani kwallo ma Najeriya lokacin gasar cin kofin duniyar da ta shige a Afirka ta Kudu.

Dan wasan na kungiyar Zaragoza ya jefa kwallonsa na farko tun bayan komowarsa fage daga mummunan raunin da ya ji a kafarsa ta hagu

Dan wasan tamaula na kungiyar kwallon kafa ta Zaragoza (a kasar Spain), Ikechukwu Uche, ya zub da hawaye yana kuka jiya laraba a bayan da ya jefa kwallonsa na farko tun komowarsa daga mummunan raunin da ya ji a guiwar kafarsa.

Wannan kwallon da Uche dan Najeriya ya jefa ya ba kungiyarsa damar doke kungiyar Athletic Bilbao da ci 2-1.

A bayan da abokan wasansa na kungiyar Zaragoza suka rufu kansa su na taya shi murnar wannan kwallo da ya jefa a minti na 55, Uche ya mike tsaye inda aka ga hawaye na zuba babu tsattsayawa daga idanunsa a bayan da ya jefa kwallon nasa na farko a kulob dinsa tun watan Mayun 2009.

Wannan shi en karon farko da aka fara buga wasa da Uche tun lokacin da aka yi masa tiyata a watan Agusta, kuma shi en karo na uku da yake buga wasa. Wasu jijiyoyi a guiwar Uche ta kafar hagu sun tsinke, abinda ya sa ya kasa buga wasa na kusan dukkan tsawon shekarar da ta shige. Da ma dai ya taba jin rauni a wannan kafa ta sa ta hagu.

XS
SM
MD
LG