Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta lallasa Mexico Da Ci 6-1 A Gasar U-17


Wani mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya
Wani mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

Kelechi Ineanacho ya jefa kwallaye har guda 4 shi kadansa a ragar 'yan Mexico a yayin da Najeriya ta kaddamar da wasan sake neman wannan kofi na duniya da ta dauka har sau 3 a baya

'Yan wasan Golden Eaglets na Najeriya sun bude wasan sake neman cin kofin kwallon kafa na duniya na samari 'yan kasa da shekara 17 tare da nunawa kasar Mexico, da ma sauran kasashen dake cikin gasar cewa Najeriya fa ba kanwar lasa ba ce idan dai batun Tamaula ake yi.

Najeriya, wadda sau uku tana cin wannan kofin, da kasar Mexico, wadda sau biyu tana lashewa, kuma ita ce ma ke rike da kofin a yanzu, sun gwabza a birnin Al Ain, a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda wannan kashi da 'yan Mexico suka sha, ya kara dulmuyar da al'amuransu ganin cewa babbar kungiyar kwallon kafar kasar ma tana fuskantar matsala a gasar share fagen cin kofin duniya ta manya.

Da farkon wasan dai, 'yan Mexico sun yi kamar zasu tabuka wani abu, amma suka kasa jefa kwallo cikin raga. da wasa yayi zafi, 'yan Najeriya sun nitsu, suka fara buga kwallo yadda ya kamata, kuma a minti na 30, Kelechi Iheanacho ya jefa kwallonsa na farko. Minti 7 bayan nan ya jefa na biyu, amma minti daya tak bayan wannan sai Mexico ta rama kwallo daya, aka tafi hutun rabin lokaci Najeriya na gaba da ci 2-1.

Komowa daga hutun rabin lokaci ke da wuya, sai Kelechi Iheanacho ya jefa kwallo na uku, inda 'yan Najeriya suka barke da sowar murna, magoya baya a cikin filin wasan kuma su na kuwwar neman kari!

Minti 3 bayan wannan kuwa, sai Chidiebere Nwakali, ya kara ma Najeriya kwallo na hudu a ragar 'yan Mexico. A minti na 60, Success Isaac, wanda yake da hannu a kwallayen da Kelechi Iheanacho ya jefa a baya, shi ma ya jefa kwallo a raga.

Iheanacho ya jefa kwallonsa na 4, wanda shi ne na 6 da Najeriya ta jefa, a ragar 'yan Mexico ana minti na 70 da fara wasan.

Yanzu dai Najeriya ita ce a saman wannan rukuni nasu na F. Najeriya zata kara da Sweden ranar 22 ga wata a nan birnin Al Ain.
XS
SM
MD
LG