Baba Shehuri, yace “mun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da wutar lantarki daga hasken rana da kamfanoni 12, don haka in an kammala zai samar da karin wutar lantarki da megawatt 1500. Ministan yace matakin ya zama wajibi don kaucewa munin tasirin illar ‘yan ta’addar Niger Delta Avengers da ke dakile kai iskar gas ga ciboyoyin samar da lantarkin.”
Za a kafa cibiyoyin samar da lantarkin daga hasken rana da zai lashe Dala Biliyan 2 da Miliyan Dari Biyar a yankin Abuja da Nasarawa da Kaduna da Sokoto da Katsina da Bauchi da Plateau.
Gwamnatin tayi maraba da kamfanin Lafarge na kamfanin siminti na Ashaka yayi azamar kafa cibiyar samar da wuta daga coal. Wannan ma’adanin dai da sauran ma’adanai na zube a garin Mai Ganga da ke karamar hukumar Akko na jihar Gombe.
Kamfanin simintin Ashaka kan shanye rabin wutar da gwamnatin Najeriya ke turawa jihohi Shida na Arewa maso Gabashin kasar, wanda ya nuna daga samun kammala kafa cibiyar wuta daga coal zai sauwake kamfanin daga dogaro ga wutar gwamnatin da ma farfadowa daga asarar da ya tafka sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka taba kaiwa kamfanin.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.