Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Saki Fursunoni 4,000 Don Sassauta Cunkoson Gidan Yari A Legas


 Gidan Yari
Gidan Yari

An saki dubban fursunoni a fadin Najeriya daga gidan yari a kokarin da ake na magance cunkoso.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya ce gwamnati ta amince da sakin fursunoni 4,068 daga cikin 80,804 da ke cikin gidajen gyara hali 253 a fadin kasar, wadanda ake tsare da su a gidan yari saboda sun kasa biyan tara.

Kakakin ma'aikatar Ajibola Afonja ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa fursunoni wadanda tarar su basu wuce naira miliyan daya ba ne kawai aka zaba don cin moriyar sakin da aka yi.

Matakin dai ya kasance wani mataki na yunkurin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda da aka zaba a farkon wannan shekarar na ganin an kawar da cunkoson gidajen yari a Najeriya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce gidajen yarin Najeriya na da cunkoson jama'a na kashi 147 a maimakon 100, kuma wadanda ake tsare da su na iya jira shekaru da dama kafin su samu damar bayyana a kotu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG