Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tayi Kira Ga Majalisar Dinkin Duniya Ta Dauki Mataki Kan Rikicin Ivory Coast


Shugabannin kasashe dake kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka,bayan taron koli na 39 d a suka yi a Abuja,ranar Laraba

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya data dauki matakan da zasu taimaka wajen magance rikicin siyasar Ivory Coast.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya data dauki matakan da zasu taimaka wajen magance rikicin siyasar Ivory Coast.

Shugaba Jonathan yayi wannan kira ne a wajen taron kolin kungiyar habaka tattalin arzikin kashen Afrika ta yamma da ake cewa ECOWAS a jiya Laraba a birnin Abujan Nigerian. Yace yana son kungiyar ECOWAS ta zartar da wani kuduri da zai bukaci Majalisar Dinkin Duniya data kara daukan wasu matakai, kodayake bai bada dalla dallan bayani akan matakan da yake son Majalisar Dinkin Duniya ta dauka ba.

To amma ya baiyana fatar cewa za’a samu hanyar magance rikicin ba tare da amfani da karfin soja. A baya, kungiyar ECOWAS tayi barazanar amfani da karfin soja, idan shugaba Laurent Gbagbo ya ci gaba da nuna taurin kai.

A ranar talata ofishin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast yace sojojin dake biyayya ga Gbagbo, suna gyara jirgin saman yaki mai saukar angulu samfurin MI-24 da kuma na’urorin harba rokoki samfurin BM21 domin amfani dasu.

Ofishin ya baiyana makaman a zaman barazana ga farar hula, kuma ya yiwa sojojin Gbagbo kashedin cewa idan suka kuskura suka yi amfani da wadannan makamai, to Majalisar Dinkin Duniya zata maida martini.

A wajen taron kolin kungiyar ECOWAS din ne kuma, wasu mata suka yi zanga zanga,kan yadda ake kashe mata a rikcin na Ivory Coast d a kuma kan wasu batutuwa da suka dami mata.

XS
SM
MD
LG