Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Bi wa Wata ‘Yar Kasarta Kadi a Ivory Coast


Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana kokarin neman belin wata ‘yar kasar, Itunu Babalola, da ke zama a kasar Ivory Coast, wadda gwamnatin kasar ta tura gidan yari har tsawon shekara 10 ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar a ranar Juma’a, karkashin hukumar da ke kula da harkokin ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje wato NIDCOM, ta ce zata bi kadin lamarin tare da nemawa Itunu Babalola, yar shekara 23 a duniya adalcin da ya dace.

Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce ofishin jakadancin Najeriya a kasar ta Ivory Coast a karkashin jagorancin Mohammed Gana, ya tura tawaga zuwa Bondoukou, birnin da ke wajen birnin Abidjan.

A halin yanzu dai, gwamnatin Najeriya na shirin tura babban lauya zuwa kasar domin nemawa Itunu Babalola hakkin ta da nuna wa kotu cewa, ba ta aikata laifin da ake zargin ta da shi ba, bayan shafe shekara 2 a kurkuku, daga cikin shekaru 10 da kotu ta yanke mata, kamar yadda sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin hukumar NIDCOM, Gabriel Odu ta bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, sabon mai gabatar da kara da aka kawo na baya-bayan nan kan shari’ar, ya bada tabbacin yin adalci ba tare da nuna son kai ba da ma yin nazari kan shari’ar domin bada belin matashiya Babalola.

Hukumar NIDCOM ta ce rahotanni da ta samu sun yi nuni da cewa, tsohon mai gabatar da kara ya hada baki da ‘yan sanda wajen sauya gaskiyar lamarin inda suka zargi Babalola da laifin safarar mutane.

An kuma yanke mata hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 20 wanda daga bisani aka rage zuwa shekara 10.

Rahotanni sun bayyana cewa, Itunu Babalola, yar asalin jihar Oyo a Najeriya, ta shafe tsawon lokaci ta na zaune a birnin Bondoukou na kasar Cote d’ivoire, kuma ta shiga wannan hali ne sakamakon zargin sata da aka yi mata inda daga bisani aka gano dan fashin dan gidan babban jami’in dan sandan caji ofis da ta kai kara ne, wanda ya yi amfani da matsayinsa wajen sauya lamarin zuwa zargin Babalola da aikata laifin safarar mutane daga bisani.

XS
SM
MD
LG