Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Yi Kokarin Ganin An Tattauna 'Yan Kungiyar Boko Haram


hotan Dorcas Yakubu wadda ke hannun kungiyar Boko Haram

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata yi kokarin ganin ta samu damar tattaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram, biyo bayan fito da wani sabon faifan bidiyo da kungiyar tayi jiya Lahadi, inda ta nuna wasu daga cikin ‘yan matan Chibok har su kusan 50 da aka kame tun a cikin shekarar 2014.

Kungiyar ta Boko Haram tace da yawan ‘yan matan sun mutu, kana sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya tayi musayar fursunoni dasu, kungiyar tace muddin ana son ta saki yan matan Chibok din to su ma a sake musu mutanen su da ake rike dasu.

A cikin faifan bidiyon na tsawon minti 11 da aka nuna ta shafin sadarwa ta Youtube an nuna wani mutum wanda ya lullube huskar sa sanye da kayan sojoji, yayin da ga wasu ‘yan mata wasu a zaune wasu kuma a tsaye.

Wasu daga cikin kalaman na wannan mutumin ko shine muddin ana son su saki ‘yan matan chibok to sai an saki ‘yan uwansu da ake tsare dasu a Maiduguri da Abuja da kuma Lagos.

Wannan bukkatar dai ba sabon abu bane da kungiyar domin ta taba yi, wannan ma yasa masu fafutukar ganin an sako wadannan ’yan matan suke cewa, ko domin wadannan ‘yan matan, lokaci yayi da gwamnatin tarayyar Najeriya zata tattauna da wadannan ‘yan Boko Haram domin ganin an saki wadannan ‘yan matan

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG