Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NATO Kungiya Ce Mai Tarin Anfani da Tasiri - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka yace Rundunar Tsaron Turai ta NATO, kungiya ce “mai tarin anfani da tasiri.”

Shugaba Obama, wanda ke kokarin kwantarda hankalin kasashen Turai dake cikin damuwa tun bayanda aka zabi Donald Trump sabon shugaban Amurka, yana wannan kalamin ne a birnin Athens na kasar Grka, daya daga cikin kasashen da yake ziyarta a balaguronsa na karshe da yake yanzu haka a kasashen duniya daban-daban.

Bayan kalaman da aka ji suna fitowa daga bakin Donald Trump da kuma wasu gwamnatocin Amurka na baya, ciki har da ta shi Obama din, Mr. Obama ya fita yaa jadadda wa kasashen Turan bukatar dada saka kudade mankuddai a aiyukkan tsaro.

Tun bayanda aka ce Donald Trump ne ya lashe zaben Amurka, shugabannin kasashen Turai da dama ke ta jiran a basu karin haske na inda aka dosa daga yanzu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG