Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Tabbatarwa Kasashen Turai Kudurin Amurka Ga Rundunar NATO


Shugaban Amurka da takwaransa na Girka
Shugaban Amurka da takwaransa na Girka

Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama yana Girka yau Talata, ya kuma kaiwa kasashen Turai tabbacin da suka dade suna jira akan kudurin Amurka ga rundunar NATO karkashin gwamnatin Donald Trump.

Kafin ya bar Amurka, shugaba Obama ya ce shugaba mai jiran gado Donald Trump, ya fada masa cewa yana da niyyar ya cigaba da huldar kawance a kungiyoyin da Amurka take ciki.

Kasar Girka ce inda shugaba Obama ya fara yada zango a ziyararsa ta karshe a matsayin shugaban kasa.
“Muna fatan yanken kasashen Turai masu karfi, da hadin kai, da cigaba ba don kawai jama’ar yankin bane amma har da sauran duniya, da kuma Amurka, a cewa shugaba Obama a lokacin da ya gayawa shugaba Prokopis Pavlopoulos na Girka jim kadan bayan isarsa babban birnin kasar.
Kafin ya bar fadar White House jiya litinin, shugaba Obama ya fadi cewa Trump ya tabbatar masa cewa yana da niyyar cigaba da mutunta kawayen da Amurka take da su cikin kungiyoyin kasa da kasa. Saboda haka daya daga cikin sakonnin da zan gabatar shine batun NATO, a cewar Obama. Shugaban mai barin gado ya fadawa kawayen Amurka dake Turai cewa babu abin da zai kawo rauni akan rawar da Amurka take takawa a NATO.
Shugabannan kasashen Turai, da suka kadu da irin kalaman Trump a lokacin yakin neman zabensa game da kudurorin Amurka, sun kagara su sami cikakken bayani.

XS
SM
MD
LG