Accessibility links

Na'urar binciken NASA ta kama hanyar zuwa duniyar Mars

  • Ibrahim Garba

Na'urar binciken duniyar Mars mai suna Curiosity

Hukumar Nazarin Sararin Subahana ta Amurka (NASA a takaice), ta

Hukumar Nazarin Sararin Subahana ta Amurka (NASA a takaice), ta kaddamar da sabuwar na’urar tafi da gidanka na binciken duniyar Mars, wadda za ta shafe shekaru biyu don zuwa da kuma bincike, kan ko akwai wasu halittu masu rai a wannan duniyar mai launin ja?

Wannan na’urar ta NASA mai kayan gwaje-gwajen kimiyya, mai suna Curiosity, wadda ta lakume kudi wajen dala miliyan dubu biyu da dari biyar, ta cilla sama a jiya Asabar a Cape Canaveral, na jihar Florida a cikin wani kunbon da babu matuki ciki.

Wannan na’ura mai girman motar safa, na da kamarori har 17, da kafafuwa masu sarrafa kansu da laser da kuma matonin duwatsun duniyar ta Mars. An yi kiyasin cewa sai ta yi tafiyar watanni 8 kafin ta isa duniyar ta Mars.

A yayin da Amurka ke murnar nasararta ta baya-bayan nan a harkokinta na sararin sama, kasar Rasha na shirn daukar mataki kan jerin cikas din da ta fuskanta a baya bayan nan.

A jiya Asabar Shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya sha alwashin daukar matakan ladabtarwa kan wadanda ke da hannu a cikas din da kasar ta fuskanta, ya na mai bayyana su da cewa munanan ‘yan mayar da hannun agogo baya ne ga kasar a fagen gasa.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG