Accessibility links

Za A Fara Babban Taron Yanayi Na Duniya a Kasar Afirka Ta Kudu


Babban taron yanayi na duniya na shekarar 2011 da za a yi a Durban kasar Afirka ta Kudu

Taron zai tattauna akan rage yawan tudadar iskar gas mai guba da kuma tsawaita yarjejeniyar Kyoto

Wakilai daga kasashe kusan maitan ne za su hallara a Durban kasar Afirka ta Kudu domin su tattauna akan dabarun shan kan canjin yanayi, a ciki har da duba yadda za a iya tsawaita yarjejeniyar Kyoto wadda wa'adin ta ya kusa cika.

Tun bayan babban taron yanayin shekarar dubu biyu da tara na Copenhagen wanda ya ci tura, an jingine kokarin samar da wata yarjejeniyar da za ta maye gurbin ta Kyoto, wadda za ta sa kasashen duniya masu ci gaban masana'antu su rage yawan tudadar iskar gas mai guba da wani adadi, nan da shekarar dubu biyu da goma sha biyu.

A muhawarorin da aka yi a baya, an yi ta mayar da hankali ne akan irin nauyin da za a dorawa kasashen da su ka ci gaba da kuma irin wanda za a dorawa sauran kasashe masu tasowa, kuma 'yan mutane kalilan ne su ka yi amanna cewa babban taron da za a fara yi a yau Litinin, zai samar da wata sabuwar yarjejeniya. Da halama dai za a tsura idanu akan manyan masu gurbata yanayi a duniya, wato Amurka da China.

A farkon wannan wata, shugaba Barack Obama ya fada cewa Amurka za ta yi amfani da taron ta bukaci kasashe masu tasowa da su ma su kara yin kokarin shan kan dumamar yanayi. Mr.Obama ya yi kashedin cewa kasashen da suka ci gaba ba za su iya yin wannan aiki su kadai ba.

Amma a wannan mako, China ta yi kira ga kasashen da su ka ci gaba cewa su taimaka wajen daukan nauyin rage tudadar iskar gas mai guba da adadi mai yawan gaske, ta ce ya kamata a yi la'akari da yadda kowace kasar da ta ci gaba ta fara gurbata yanayi tun shekaru dari biyun da suka gabata, sannan kuma ta ce kasashe masu tasowa ba su da arzikin daukan matakai iri daya da kasashen da su ka ci gaba.

Amurka ba ta taba amincewa da yarjejeniyar Kyoto ba, kuma ta dage cewa duk wata yarjejeniyar da yin aiki da ita ya zama wajibi, to lallai ne ta hada har da kasashe masu tasowa.

Haka kuma babban taron zai duba yiwuwar tara dola miliyan dubu daya a kowace shekara da za a zuba a gidauniyar yaki da canjin yanayi, wadda aka girka da nufin taimakawa kasashe su iya tinkarar matsalar dumamar yanayi.

Irin hadirin yashin da canjin yanayi ke jawowa a kasashen Sahel irin su jamahuriyar Nijer
Irin hadirin yashin da canjin yanayi ke jawowa a kasashen Sahel irin su jamahuriyar Nijer

XS
SM
MD
LG