Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Navarro Ya Ce Karin Kudin Fito Kan Karafa da Tama Na Amurka Ba Zai Bar Kowa Ba


Peter Navarro mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin kasuwanci da cinikayya

Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara a kan harkokin cinikayya Peter Navarro ya fada jiya Lahadi cewa shugaban na Amurka ba ya da niyyar cire ko wace kasa daga karin kudin fito na shigo da tama da karafa daga kasashen ketare.

Peter Navarro ya fada wa gidan telebijin na CNN cewa za a fitar da cikakken bayanin kasashe da ake sa ran zasu rika biyan kashi 25 cikin 100 na kudin fito kan tamar da zasu kawo Amurka, da kuma kashi 10 na kudin karafa a wani lokaci cikin wannan satin ko kuma farkon sati mai zuwa.

Sai dai wannan sabon tsarin kudin fiton da shugaba Trump ya fito da shi akan muhimman karahuna yayi karo da suka daga wasu ‘yan majalisar jam'iyyarsa ta Republican masu nasaba da harkokin kasuwanci har ma da sauran takwarorin kasuwancin Amurkan irin su Canada dama kungiyar tarayyar Turai.

Sai dai Navarro yace ana bukatar wannan kudin fiton ne domin kare harkokin tsaron Amurka da kuma na tattalin arzikin ta.

Navarro yace shugaban na Amurka ya saurari dukkan bangarori biyu masu ra'ayin da suak sha bambam a kan wannan batu kafin ya kai ga tsaida wannan shawarar. Yace zai zamo rashin dabara idan aka ce za a kara kudin fito a kan wasu kasashe ne, yayin da za a tsame wasu daga biyan wannan karin kudin fito. Yace za a samar da wasu hanyoyi da za a bi domin tsame wasu kamfanoni na cikin kasa daga biyan farashi mai tsada na wadannan karafa da aka shigo da su, bisa la'akari da yanayin da suke ciki.

Musali kasar Canada wacce take tafi kowace kasa kasuwanci da Amurka, ita ce wannan lamarin zaifi shafa domin ko a shekarar da ta gabata ta sayarwa da Amurka karfen goran ruwa na dala miliyan dubu 7 da 200, da kuma tama ta dala miliyan dubu 4 da 300. Haka kuma wannan karin kudin fiton zai shafi wasu kawayen na Amurka, irin su Birtaniya, Jamus, Koriya ta Kudu, Turkiyya da Japan. Amma China da take tafi duk wata kasa a duniya samar da tama, tana sayarwa da Amurka kashi 2 cikin 100 ne kawai na irin tamar da take samarwa, don haka lamarin ba zai shafe ta sosai ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG