Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kare Shirin Saka Haraji Kan Karafan Waje


Sugaban Amurka Donald Trump
Sugaban Amurka Donald Trump

Yayin da ake fargabar yiwuwar fuskantar gasa a kasuwannin duniya sanadiyyar sa haraji da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi kan karafan kasashen waje, Trump ya kare matsayinsa

Yau Jumma’a Shugaban Amurka Donald Trump ya kare aniyarsa ta saka haraji mai tsanani kan karafan da ake shigo da su daga kasashen waje, inda ya ce gwagwarmayar cinakayyar da ka biyo baya, za ta iya amfanar Amurka.

“Muddun kasa (kamar Amurka) na asarar biliyoyin daloli a huldar cinakayya da kusan kowace kasa, to ya kamata a shiga gasar cinakayya, kuma ta na da saukin sha’ani,” abin da Trump ya rubuta Kenan ta kafar Twitter. Ya kara da cewa, “Misali, idan mu ka yi asarar biliyan 100 wajen cinakayya da wata kasa, ita kuma ta amfana sosai, to a daina wannan cinakayyar – za mu amfana gaya. Shi ne ma ya fi sauki!.”

Shirin kara harajin na Trump, wanda aka sanar kwana guda gabanin nan, ya jenyo fargabar gasar cinakayya, a yayin da wasu kasashen ke sayarwa da arha kuma shugabannin wasu kasashen kuma ke barazanar mai da martani.

Yau Jumma’a farashen Nikkei na Japan ya yi faduwar tsawon sama da mako guda. Ya fadi da kashi 2.5% zuwa maki 21,181.64, wanda bait aba faduwa haka bat un daga 14 ga watan Fabrairu.

Yau Jumma’a China ta nuna matukar damuwa kan wannan salon cinakayya ta ta Amurka, to amma ba ta mai da martani nan da nan kan wannan sanarwa ta Trump ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG