Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDLEA Ta Kama Wasu Mata Masu Safarar Miyagun Kwayoyi A Jihar Benue


Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa (Twitter/ NDLEA)

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) sun yi nasarar kama wasu mata biyu wadanda ake zargi da saffarar miyagun kwayoyi.

Nau'in kwayoyin da aka kama su da shi sun hada da na Diazepam da Exol-5 wadanda adadinsu ya kai dubu 296,000.

An kama su ne a lokalin suna kan hanyarsu ta zuwa Gombe daga jihar Anambra.

Rahotonnin sun yi nuni da cewa an kama Chioma Afam mai shekaru 36 da haihuwa bayan canja sunanta da ta yi a lokuta da dama zuwa Amina da Uzoamaka da Ifunaya don boye miyagun ayyukan da ta ke aikatawa.

Jami'an star sun bayyana sunan daya matar a matsayin Chidinma Caleb 'yar kimanin shekaru 22. Dukkansu matan biyu an kama su ne sanye da hijabi a matsayin wata dabara ta boye kamininsu .

A cewar hukumar ta NDLEA, nasarar kamen ya zo ne sa’ilin da jami’an hukumar da ke gudanar da ayyukan bincike na motocin dake wucewa ta babbar titin Makurdi na jihar Benue, inda aka tsare motar da matan suka shiga daga garin Onitsha na jihar Anambra don zuwa jihar Gombe.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG