Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Yi Hobbasa A Yaki Da Miyagun Kwayoyi


Hukumar Yaki Da Miyagun Kwayoyi ta NDLEA

Damuwar da hukumomi ke yi sakamakon karuwar amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya, ya sa hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa ta (NDLEA) ta bayyana aniyarta ta bude dakunan gwaji a jihohi 36 na tarayya.

Shugaba kuma babban jami’i a hukumar yaki da miyagun kwayoyin, Brig General Buba Marwa, da babban darektan hukumar ya wakilta ya bayyana wannan batu a wata takarda zuwa ga kwamitin yaki da miyagun kwayoyi a Majalisar Dattawa a ranar Alhamis a wani sauraren bahasi na bainar jama’a.

Kwamitin yaki da miyagun kwayoyin na Majalisar Dattawa ya gudanar da wani sauraren bahasi na jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin yi wa dokokin miyagun kwayoyi na shekarar 2004 gyarar fuska a cikin wani kuduri na shekarar 2021.

Shugaban kwamitin, Sanata Hezekiah Ayuba Dimka, ya yi alkawarin gaggauta fitar da sakamakon sauraren bahasin, ya na mai cewa dokokin miyagun kwayoyi na bukatar cikakken garanbawul domin hukunta wadanda za su take dokar.

Shugaban kwamitin ya ce sashe na hudu na ainihin dokar dake kula da ikon da hukumar ke aiki da ita, ya bada damar yin gyara, dalilin haka ne kuma ake wannan gyarar fuska da zai bada ikon kafa dakunan gwaji a jihohi 36 na kasar da kuma Babban Birnin Tarayya.

Ya ce “Sashen na hudu na babbar dokar ya ba hukumar wani iko na musamman da yake bada hurumin saka wasu kananan sassa a dokar.”

Ya kuma ce hukumar ta NDLEA za ta samu karfin gudanar da bincike cikin gaggawa kana ta gabatar da batutuwan muggan kwayoyi gaban kotu idan akwai dakunan gwaji a fadin kasar.

Ya yi kira ga Majalisar Dokokin Kasa da ta yi la’akari da kasafin kudin hukumar domin ta iya samun isassun kudade da za ta samu kayan aikin.

XS
SM
MD
LG