Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEJA: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Mutane Ta Hanyar Banka Masu Wuta A Rami


Ramin da aka kona wasu mutane
Ramin da aka kona wasu mutane

Bayan kubutar da yan kasar China 7 da yan bindiga suka sace a jihar Neja, 'yan bindiga sun kashe wasu mutane 7 ta hanyar banka masu wuta a rami a jihar Neja.

Hukumomi a Nigeria sun bayar da tabbacin kubutar da wasu 'yan kasar China su 7 da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da su a jihar Neja.

Tun a cikin watan Yunin da ya gabata ne dai 'yan bindigar suka aukawa 'yan kasar Chinan a wani wurin hakar ma’adanan karkashin kasa da ke yankin Shiroro, mai fama da 'yan bindiga da hukumomin jihar su ka ce mayakan kungiyar Boko Haram ne.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Mr. Emmanuel Umar kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Nejan, yace an samu nasarar kubutar da 'yan Chinan ne a sakamakon hare haren da gamayyar jami’an tsaron Nigeria suka kai wa 'yan ta’addan a maboyarsu.

Sai dai a yayin da aka samu Nasarar kwato wadannan 'yan China, rahotanni daga yankin na Shiroro na nuna cewa, 'yan bindigar sun hallaka wasu mutanen 7 ta hanyar tura su rami sannan suka banka masu wuta a ranar Asabar din nan ta karshen mako.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar 'yan sanda ta jihar Neja akan wannan sabon hari.

Kwamishin tsaron cikin gida na jihar Emmanuel Umar yace gwamnati na kokarin kawar da wadannan mahara da suka addabi jama’a.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG