Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Wasu Da Ake Zargin 'Yan ISWAP Ne Sun Kashe Sojoji Da Farar Hula


Wasu motoci da aka kona a sansanonin sojoji
Wasu motoci da aka kona a sansanonin sojoji

Wadansu ‘yan bindiga sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke wani gari a arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe sojoji tara da ‘yan sanda biyu da fararen hula a ranar Lahadin da ta gabata a cewar majiyoyin tsaro da mazauna yankin, a wani sabon rikici da ya barke a yankin.

A wani hari da aka kai wa sansanin da garin a ranar Asabar, 'yan bindigan sun jefa bama-bamai tare da kashe mazauna garin, yayin da wasu kuma suka nutse a cikin kogin da suke kokarin gudu.

Majiyoyin tsaro biyu sun tabbatar da cewa harin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata inda aka kashe sojoji tara da ‘yan sanda biyu a sansanin.

A yayin da suke tafiya cikin manyan motoci masu hade da bindiga, mayakan, wadanda ake zargin 'yan kungiyar IS ne a yankin yammacin Afirka (ISWAP), sun kai farmaki a garin Malam Fatori da ke gundumar Abadam, da yammacin Juma'a da safiyar Asabar, in ji su.

"Yan ta'addar ISWAP sun kai wa Malam Fatori hari inda suka yi barna mai yawa wanda muke cikin aikin tantancewa," wani jami'in soja ya shaida wa AFP.

“Sun kai hari a sansanin soji kuma sun yi artabu da sojoji yayin da wata kungiya ta biyu ta kai harin kashe-kashe da kone-kone a garin,” in ji jami’in da ya nemi a sakaya sunansa.

Harin farko da aka kai a kusa da kan iyaka da Nijar, ya zo ne da yammacin ranar Juma'a, wanda ya kai ga gwabza kazamin fada da sojojin da suka dakile harin, in ji Buji Garwa mazaunin garin.

“Wadanda suka mutu a sansanin sun kai 11, ciki har da sojoji tara da ‘yan sandan tafi da gidanka guda biyu da ke aiki tare da sojoji,” in ji wani jami’in soja.

Wata majiyar tsaro ta biyu ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Mun rasa sojoji tara da ‘yan sanda biyu daga sansanin, har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kashe a cikin garin ba,” in ji majiyar tsaron.

“Ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe ba saboda dukanmu mun gudu daga garin kuma a hankali muke komawa don tantance irin barnar da aka yi.” Inji Garwa. Ya kara da cewa an kona yawancin garin.

“Mun fara tantacce dazuzzuka tare da kwasan gawarwakin wadanda aka kashe,” inji shi.

A cewar wani jami'in leken asiri, maharan sun fito ne daga kauyen Kamuya dake kusa da wurin.

“Kamuya shi ne sansanin ISWAP mafi girma a yankin tafkin Chadi wanda ke da tazarar kilomita 8 daga Malam Fatori,” inji majiyar.

Ya kara da cewa, “Dukkan hare-haren da aka kai wa Malam Fatori a baya wanda bai yi nasara ba, an kaddamar da su ne daga Kamuya, wanda ke da katanga da nakiyoyi da manyan makamai."

Mayakan Boko Haram sun kwace Malam Fatori, mai tazarar kilomita 200 daga babban birnin yankin Maiduguri, a gefen tafkin Chadi, a shekarar 2014 amma sojoji sun yi masa kawanya a shekarar 2015.

An kafa wani sansani a garin domin dakile hare-haren ISWAP, wacce ta balle daga Boko Haram a shekarar 2016, ta mayar da tafkin Chadi wani sansani.

A cikin watan Maris din da ya gabata ne aka mayar da dubban mutanen da suka yi gudun hijira zuwa Maiduguri, inda aka mai da su Malam Fatori bisa umarnin gwamnatin jihar Borno, duk kuwa da cewa kungiyoyin agaji sun nuna damuwar hakan.

Rikicin dai ya barke ne tun a shekarar 2009 kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu.

XS
SM
MD
LG