Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neymar Ya Gama Jiyyar Coronavirus


Dan Wasan PSG Neymar

Neymar ya dawo daga jiyyar cutar coronavirus, a yayin da kungiyarsa ta PSG ta ke shirin buga wasan farko ta bude gasar League 1 ta sabuwar kakar wasanni.

Shahararren dan wasan kasar Brazil Neymar ya koma taka leda a kungiyarsa ta PSG, inda ake sa ran zai buga wasan farko ta gasar Ligue 1 ta sabuwar kakar wasanni da Marseille a gobe Lahadi, bayan fitowa daga killacewar cutar COVID-19.

An auna tare da tabbatar da Neymar ya kamu da cutar a ranar 2 ga watan nan na Satumba sa’adda yake hutu a Ibiza, bayan kashin da kungiyar sa ta sha a hannun Bayern Munich da ci 1-0 a wasan karshe ta gasar Zakarun Turai.

Dan Wasan PSG Neymar
Dan Wasan PSG Neymar

An killace Neymar, da ma wasu takwarorinsa ‘yan wasan PSG din kamar Kylian Mbappe, Angel Di Maria da Leandro Paredes sakamakon kamuwa da cutar.

PSG ta ba da sanarwar karin ‘yan wasanta 3 da suka kamu da cutar; dan kasar Argentina Mauro Ikardi, da dan kasar Brazil Marquinhos da kuma mai tsaron gida Keylor Navas.

Bayan fafatawa da Marceille a gobe Lahadi, PSG din za ta buga da Metz a ranar Laraba, kafin kuma ta kara Nice a ranar Lahadi ta mako mai zuwa.

Facebook Forum

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG