Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Nawa Ne Harin Bama Bamai Ya Halaka A Abuja?


Wata mace wacce ta rasa dan'uwa a tashin Bam a Abuja,tana kuka ne a babban asibitin Asokoro dake Abuja,ranar jumma'a 31 ga watan Disemba.

Jami’an Najeriya sun bada labarin bam ya tashi cikin wata sananniyar kasuwa dake kusa da wani barikin soja cikin birnin Tarayya Abuja.

Jami’an Najeriya sun bada labarin bam ya tashi cikin wata sananniyar kasuwa dake kusa da wani barikin soja cikin birnin Tarayya Abuja.

Wani kakakin ‘yansanda yace mutane hudu ne tashin bam din ya halaka,13 kuma suka jikkata.Tashar talabijin ta kasar NTA tace mutane 30 ne suka halaka.

Babu tabbas kan wan nan rahoto. Jami’ai suka ce bam din ya tashi ne cikin wata kasuwar da mutane suke bukukuwan shiga sabuwar shekara.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yana zarfin kungiyar Boko Haram da kai wan nan hari.

Wan nan kungiyar din ce dai ta dauki alhakin kai haria Jos a jajiberen kirsmimeti,da wadanda aka kai kan wadansu majam’u da dama abvirnin Maiduguri. Fiyeda mutane 80 ne suka halaka a wadan nan hare hare.

XS
SM
MD
LG