Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Mai Tsattsauran Ra'ayin Islama a Nijeriya ta Yi Ikirarin Kai Hare Hare a Nijeriya


Harabar Majami'ar Victory Baptist da aka kai wa hari a Maiduguri a ranar jajebirin Kirsemati kenan

Wata Kungiya mai tsattsauran ra’ayin Islama a Nijeriya, ta ce ita ce ta kai hare-haren ranar jajebirin Kirsamati, wadanda su ka hallaka a kalla mutane 86.

Wata Kungiya mai tsattsauran ra’ayin Islama a Nijeriya, ta ce ita ce ta tayar da bama-bamai ta kuma kai hare-haren ranar jajebirin Kirsamati, wadanda su ka hallaka a kalla mutane 86.

Kungiyar ta Boko Haram ta ce za ta cigaba da kai hare-hare kan wadanda ta kira, marasa imani.

Hukumomi a Nijeriya sun ce mutane akalla 80 sun mutu a garin Jos da ke tsakiyar kasar, inda aka auna bama-bamai kan masu sayayyan karshe na bikin Kirsamati.

A wannan ranar ce kuma, aka kai hare-hare kan wasu Majami’u a birnin Maiduguri na Arewacin Kasar, inda aka kashe akalla mutane shida.

Hare-haren sun tayar da tashe-tashen hankula a Jos ranar Lahadi tsakanin Musulmi da Kirista. An banka wa gine-gine da dama wuta a lokacin yamutsin kuma ‘yan sanda sun ce sun damke a kalla mutane uku.

Gwamnatin Nijeriya dai ta ce wannan yamutsi na baya-bayan nan an tayar da shi ne da manufa ta siyasa, da zummar kawo zaman dar-dar tsakanin Musulmi da Kirista kafin zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Afrilu.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin farauto wadanda su ka kai harin bama-baman jajebirin ranar Kirsamatin.

XS
SM
MD
LG