Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Tsaro Ta Najeriya Ta bada labarin Kama wani Akwatin jigilar Kaya ta Ruwa da Makamai da suka hada da Gurneti Gurneti da Wasu Makamai


Kakakin hukumar, Marilyn Ogar ce ta bayyana haka Talata,kuma ta ce jami'an hukumar suna bincike domin gane sauran makamai. Shi wan nan akwatin an lika masa shaidar yana dauke da kayan gini.

Jami’an hukumar tsaro, farin kaya a Najeriya,sun bada labarin kama wani akwatin kaya na jirign ruwa dauke da makaman gurneti da wasu nakiyoyi,a tashar jiragen ruwa dake Legas.

Kakakin hukumar Marilyn Ogar, ce ta bayyana haka yau talata, ta kara da cewa jamai’ai suna binciken wasu akwatunan da ake tsammanin suna dauke da makamai. Ogar tace akwatin da aka kaman an lika masa shaidar cewa yana dauke ne da kayan gine gine.

Sai dai taki ta fadi daga inda aka turo kontenar kuma ina ya dosa a Najeriya. Jami’an tsaro cikin kasar suna cikin shirin ko ta kwana,tun harin boma bomai kusa da inda aka yi bikin ranar samun ‘yancin kai,daya ga watan Oktoba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG