Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya Sun Tsananta Matakan Tsaro ta Ruwa da Sama da Kuma ta kan iyakokin kasar,Bayan Kama Akwatuna Shake da Makamai


Wani soja yake nuna hanu a lokacinda suke nunawa manema labarai gungun makamai da jami'an tsaro suka kama a wata tashar jiragen ruwa ranar Talata da ta shige.

An kara daukan karin matakan tsaron ne bayan da jami'an kasar sun kammala wani taro da suka yi ranar Alhamis a birnin Abuja,babban birnin kasar.

Jami’an Najeriya sun tsananta matakan tsaro a tashoshin jiragen ruwa da na sama da ma akan iyakokin kasar,bayan kama akwatuna cike da makamai a wata tashar jiragen ruwa a Legas cikin makon.

Kara daukan wadan nan matakan tsaron, ya biyo bayan wani muhimmin taro da shugabannin kasar suka yi jiya a Abuja.

Ranar Talata ce jami’an tsaro suka kama akwatuna masu yawa cike da makamai d a suka hada da gurneti,nakiyoyi,da rokoki. Zuwa yanzu dai hukumomin Najeriya sun kama mutane biyu dangane da wan nan lamari.

Tun ranar daya ga watan Okotoba ne jami’an tsaron kasar suka zabura haikan bayan wani harin boma boma a babban birnin kasar da ya kashe mutane 12. Kungiyar tsagerun yankin Niger Delta (MEND) ta dauki alhakin kai wan nan hari.

XS
SM
MD
LG