Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi A Hotel Na Gwamnati A Jihar Delta A Kudancin Najeriya


Tashin bam wanda tsageran Niger Delta suka dauki alhakin dasawa cikin mota ranar 1 Oktoba, 2010 a Abuja, babban birnin Najeriya

Wannan bam bai yi kisa ba, amma ya lalata dakuna biyu a masaukin gwamnati dake Asaba, babban birnin Jihar Delta a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Bam ya tashi cikin wani hotel mallakar gwamnati a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kudancin Najeriya.

Wannan bam da ya tashi jiya laraba bai kashe kowa ba, amma kuma ya lalata dakuna biyu a gidan saukar bakin gwamnati dake Asaba, babban birnin Jihar Delta. ‘Yan sanda sun ce su na binciken wannan lamarin.

Tsagera a yankin Niger Delta, wadanda suka ce sun fusata da gurbatar yanayi da talauci da ake fama da shi duk da irin dimbin arzikin dake wannan yanki, sun yi ta kai hare-hare na farfasa bututun mai tare da sace ma’aikatan mai ‘yan kasashen waje a cikin yankin.

Akasarin wannan tashin hankali ya tsaya a bayan da aka cimma yarjejeniyar yin ahuwa a tsakanin gwamnati da shugabannin tsageran.

Amma a watan da ya shige na Oktoba, wani harin bam da aka dasa cikin mota, wanda kuma tsageran na Niger Delta suka dauki alhakin kaiwa, ya kashe mutane 10 a Abuja, babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG