A jamhuriyar Nijar an fara gudanar da taron matan jam’iyyun siyasun kasashen Afirka masu ra’ayin gurguzu, domin nazarin hanyoyin magance matsalolin da suka addabi mata, wadanda suka hada da batun rike mukamin shugabancin siyasa da maganar noma.
Haka zalika, a tsawon kwanaki biyu na wannan taro mahalartan za su nazarci matakan murkushe wata mummunar al’ada dake zama ruwan dare a wasu kasashen Afirka.
Ministar kare hakkokin mata Madam Elback Zeinabou Tari Bako tace babban burin da aka sa gaba a karkashin wannan haduwa shine samar da hanyoyin da zasu kawo karshen rashin adalcin, da jinsin mata ke fuskanta a nahiyar Afirka.
Domin jaddada matsayinsu matan jam’iyyun siyasa masu akidar gurguzu zasu fitar da wata sanarwar a karshen taron mai kunshe da jerin bukatun mata.
Da suke jawabi a yayin bukin bude wannan taro, magatakardar kungiyar jam’iyyun siyasa masu ra’ayin gurguzu a duniya Luis Ayala, da shugaban jam’iyyar PNDS Tarayya mai masaukin baki wato Bazoum Mohamed, sun jaddadawa matan cikakken goyon baya da zasu basu don samun nasara.
Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 30, 2023
Kamala Harris Ta Gana Da Mata ‘Yan Kasuwa Na Kasar Ghana
-
Maris 29, 2023
Zimbabwe Na Duba Yiwuwar Soke Hukuncin Kisa
-
Maris 29, 2023
Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.
Facebook Forum