Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Bukin Karrama Dalibai Masu Kwazo Da Hazaka A Fannin Kimiya


Dalibai a Nijar

A Jamhuriyar Nijar shugabar gidauniyar Guri wato uwargidan shugaban kasa Hajiya Aichatou Issouhou Mahamadou, ta jagoranci bikin karrama wasu dalibai sama da 200 da suka fi nuna kwazo, da hazakar karatu a fannin ilimin kimiya.

Wannan shine karo na tara da ake shirya irin wannan buki na bayar da tukwici da lambobin yabo ga daliban da suka fi abokansu hazakar karatu, da nufin cusawa matasan Nijar kwadayin romon dake tattare da ilimin zamani.

Ousman Kadri Nouhou shine daraktan zartarwar gidauniyar Guri Vie Meilleur wace ke dauke da dawainiyar wannan tsari mai sunan Prix de l’Excellence et du merite.

Samarwa Nijar wadatattun ma’aikatan da suka kware a fannonin dake ciyar da kasa gaba, na daga cikin abubuwan da gidauniyar Guri Vie Meilleur ke hange a karkashin wannan tsari na karrama daliban makarantun boko, inji shugabar wannan gidauniya uwargidan shugaban kasar Nijar Hajiya Aichatou Issouhou Mahamadou.

'Yaran da suka yi nasarar shiga sahun hazikan daliban wannan shekara sun samu tukwici kala kala masu tsoka, abin da ake ganin zai iya sassauta wahalhalun iyayen yaran, da abin ya shafa.

Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma, ya zanta da wasu daliban da suka je Yamai takanas daga jihohi domin karbar nasu tukwicin.

A yammacin yau Laraba shugaban kasa Issouhou Mahamadou ke karbar wadanan dalibai a fadarsa domin yi masu gargadi akan bukatar su maida hankali akan karatu, yayin da su ma malaman makarantar da aka baiwa lambar yabo saboda kwarewa da gwada kishi akan aiki zasu samu jinjina daga gareshi.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG