Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Jamiyyun Siyasa sun amince da rajistan sunayen masu jefa kuri'u


Mr.Morou Amadou, ministan shari'a na kasar Nijar
Mr.Morou Amadou, ministan shari'a na kasar Nijar

Biyo bayan kwaskwarima da aka yiwa rajistan sunayen masu jefa kuri'u na jamhuriyar Nijar, yanzu dai duk jam'iyyun da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a zaben kasar da za'a yi watan gobe sun amince da kundun.

Da yammacin Alhamis ne kwamitin da ya kunshi jam'iyyun siyasa da wasu kungiyoyin ya gabatar da kundun rajistan masu kada kuri'u kuma dukansu suka yi amanna dashi.

Rabilu Alhaji Kani yayi magana da jam'iyyar MNSD Nasara yace hakarsu ta cimma ruwa. Tun farko sun yi korafin cewa kundun ya kunshi sunaye jabu. An bincika kuma an fitar da sunaye jabun, saboda haka sun amince. Yanzu sai 'yan kasa su je su yzabi shugabanni da Allah zai sa su zama alheri ga kasar yaddako mutum ya sha kaye zai yadda ba tare da hamayya ba..

A can baya bangaren rinjaye ya fuskanci zargi ba iyaka daga 'yan hamayya akan cewa yayi kakagida akan ayyukan fark farkon rajistan sunayen masu zaben.

Bubakar Sabo sakataren jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki yace cire sunayen mutane da dama daga kundun ba zai shafi nasararsu ba. Yace 'yan adawa ne suke korafi amma su basu da wata matsala domin su ne kan gaba a koina acikin kasar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG