Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Kotu Ta Bada Belin Dan Hamayya Ali Tera


Kotun Nijar
Kotun Nijar

An tsare dan gwaggwarmayar ne a gidan yarin Koutoukale saboda zarginsa da yunkurin tunzura jama’a da nufin kifar da zababbiyar gwamnati har ma da zargin barazanar kisan shugaban kasa na wancan lokaci.

Ana zargin Ali Tera da amfani da hanyar sakwannin bidiyo da maganganun da ya ke yadawa a kafafen sada zumunta daga birnin New York inda yake zaune yana caccakar kamun ludayin shugaba Issouhou Mahamadou har ma da dura masa ashar da nufin nuna rashin gamsuwa da mulkinsa.

NIGER: 'Yan adawa dake kurkuku a Nijar
NIGER: 'Yan adawa dake kurkuku a Nijar

Lamarin wanda ya faro a wajejen karshen shekarar 2014 yazo karshe a shekarar 2018 lokacin da gwamantin jamhuriyar Nijer ta yi sa’ar karbo shi daga hannun hukumomin Amurka inda kai tsaye aka wuce da shi gidan yarin Koutoukale dake matsayin gidan ajiyar gaggan ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifika.

Bayan shafe watanni sama da 30 a kurkuku wani alkalin kotun Yamai ya bada belinsa a yammacin jiya litinin kamar yadda lauyan Ali Tera Me Mossi Boubacar ya yi min Karin bayani.

A hirar shi da Muryar Amurka, lauyan yace wa’adin da doka ta kayyade ya riga ya shude tun tuni domin doka tace ko kisan kai mutun ya yi bai kamata ya wuce wata 18 ba a tsare ba tare da alkali ya saurare shi ba. kuma ko da za a sake tsawaita zamansa a gidan yari doka tace sau 1 za a tsawaita shi kuma kada zaman ya wuce watanni 12 kawai, amma Ali Tera ya shafe watannin sama da 30 a kulle ba tare da an yi masa shara’a ba dalili kenan alkali ya amincewa bukatarmu ta bada belinsa.

NIGER: 'Yan adawa dake kurkuku a Nijar
NIGER: 'Yan adawa dake kurkuku a Nijar

Ali Tera wanda a wani lokacin baya ke bayyana kansa a matsayin dan jam’iyar Moden Lumana ta ‘yan hamayya, ya yi tsayin daka a wancan lokaci domin fito na fito da duk wanda ke sukar manufofin jam’iyar ta tsohon fira Minista Hama Amadou.

Matakin sallamar dan gwaggwarmayar wani abu ne da wasu ‘yan kasa ke kallonsa a matsayin wata alamar sauye sauyen da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi alkawali aiwatarwa a fannin shara’a inda jama’a ke kokawa game da yadda ake fuskantar tsaiko kafin a saurari wanda ake tuhuma da aikata laifi kamar yadda kungiyar alakan shara’a ta sha korafi akan yadda wasu masu bakin fada a ji ke fakewa da matsayinsu don katsalandan a harakokin shara’a.

matakin-kama-ali-tera-ya-janyo-muhawara-a-nijer

yan-adawa-a-jamhuriyar-nijar-sun-zargi-hukumomi-da-tsangwamar-su

nijar-yar-jaridar-da-hukumomi-suka-kama-ta-gurfana-a-gaban-kotu

Saurari cikakken rahoton da Souley Moumouni Barma ya aiko mana:

An bada belin Ali Tera:3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG