Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Ma'aikatan Ofishin Magajin Gari Sun Ki Janye Barazanar Yajin Aiki


Wasu Ma'aikata Da Suka Yi Zanga Zanga a Nijar

A Jamhuriyar Nijar jami’ai a ma’aikatar magajin garin birnin Yamai sun kudiri aniyar shiga yajin aiki na kwanaki biyar daga ranar litinin mai zuwa da kuma yin wani jerin gwano sakamakon shafe watanni bakwai da suka yi ba tare da an biya su albashi ba.

Jami’ai sama da dubu dake karkashin hukumomin birnin Yamai ne ke fama da wannan matsalar rashin albashi wadanda a cewarsu rabonsu da albashi tun watan Yuni na 2016, saboda abinda ma’aikatar magajin gari ta kira rashin kudi a aljihun gwamnati.

Rashin fahimtar da aka samu tsakanin hukumomi da shugabanin ma’aikata a tattaunawarsu ta baya-bayan nan, ta sa shuwagabanin kungiyar kwadagon kiran taro domin sanar da magoya bayansu halin da ake ciki domin sake duba hanyar da za su bullowa al'amarin.

Malam Hassan Jawondo Usman, daya daga cikin shuwagabanin ma’aikatan, ya ce tattaunawar da aka yi, ba ta yi wani armashi ba domin kudin wata daya ne kawai aka amince za a biya su.

A karshen taron daukacin ma’aikatan da suka hada da masu aiki a ofisoshi da masu gadi da masu aiki a wajan ajiya da dai sauransu sun yanke shawarar ci gaba da yin gwagwarmaya har sai haka ta cimma ruwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG