Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Masu Noman Zogale Sun Dauki Matakin Yaki Da Kwararowar Hamada


Wata mace a gonar zogale (Lisa Bryant/VOA).
Wata mace a gonar zogale (Lisa Bryant/VOA).

Masu ruwa da tsaki a kasuwanci da noman zogale sun fara wani zama don nazarin hanyoyin saka tsari a wannan fanni da ke samar da kudaden shiga ga dimbin ‘yan kasar musamman mata.

Noman zogala ya zama wata hanyar yaki da kwararowar hamada da ma yaki da cutar Tamoa a wajen yara kanana abinda ya sa hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO ta kudiri aniyar bada tallafin makuddan kudade don bunkasa wannan fanni.

Lura da yadda kasuwanci da noman zogala ke gudana cikin yanayi irin na kara zube ya sa hukumomin Nijer bullo da shirin saka tsari a wannan fanni ta yadda za a bunkasa harkokin dake da alaka da noman zogala ta hanyar abinda ta kira makon musamman dake tattara manoma da masu kasuwancin zogala da kwararru a fannin kare muhallI.

Ba ya ga batun yaki da kwararowar hamada Yaki da talauci da yaki da cututukan dake da nasaba da karancin abinci mai gina jiki a wajen yara na daga cikin abubuwan da gwamnatin wannan kasa ta sa gaba a karkashin wannan shiri.

A tsawon wannan mako masu ayyukan sarrafa zogala zasu baje kolin nau’oin abubuwan da suke samar wa a matsayin wata gasar gwada fasaha wace ka iya zama wata hanyar jan hankulan jama’a a game da mahimmancin wadanan albarkatu.

Da yake jawabi a yayin bukin soma wannan zama na makon musamman wakilin hukumar samar da abinci ta duniya a Nijer Attaher Maiga ya jaddada goyon bayan hukumar ta FAO don ganin gurin bunkasa noman zogala ya cika cikin dan kankanen lokaci.

Gwamnatin Nijer ta bayyana cewa daga yanzu ta kudiri aniyar bai wa noman zogala mahimmanci kasancewarta hanyar ayyukan farfado da kasar noma sannan wani shige na yaki da kwararowar hamada yayinda a fannin tattalin arziki kasar ke fatan ganin an samu kudaden shiga kwatankwacin yadda wasu kasashen ke alfahari da noman coco.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG