Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Na Shirin Fassara Kundin Tsarin Mulkinta Zuwa Wasu Harsunan Kasar


Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed

A wani yunkuri na wayar da kan al'uma domin su kara fahimtar muhimman dokokin dake kunshe a kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, har ma da muhimman dokokin kasa da kasa, kungiyar masanan doka ANC ta cimma yarjejeniya da ma’aikatar fassara ta CCL Nijar domin fassara wadanan dokoki a cikin wasu harsunan kasar.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa kusan kashi 80 cikin 100 na al’umar Jamhuriyar Nijar, ba su da masaniya kan abinda ya kundin tsarin mulkin kasar ya kunsa.

Hakan ya sa hukumomin kasar suka hada kuduri aniyar fassara muhimman dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.

A cewar Darektar ma’aikatar fassara ta CCL a Nijar, Hajiya Fatima Sahabi, “a cikin tsarin mulkin dimokradiyya muke, ya kamata a ce kowane ya san menene kundin nan ya kunsa.”

“Za mu fassara su a harshen Hausa da Zabarbanci da da Kanuri a bugu na farko abinda muke nufi a nan shine karfafawa da sanin demokradiyya da doka, wadannan abubuwa idan an san su za su kawo ci gaba.” In ji Dr. Maina Bukar Karte na kungiyar ANC mai dauke da masana doka.

Ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakuba ya nuna farin cikinsa kan tabbatuwar wannan aiki zai kara tabbatar da daidaituwar tafiyar mulkin demokradiyya a kasar.

“Yana da muhimmanci a ce cikin demokradiyya a ce mun cimma wannan nasar wadanda suke jin harshen da ba turanci ba a ce sun san mai kundin nan ya kunsa sun kuma san mai dokoki suka kuna.”

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG