Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kamaru 34 Sun Yi Batan-Dabo


Wasu daag cikin dakarun kasar Kamaru yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya

Ma’aikatar tsaron Kamaru ta fada a yau Litinin cewa sojojinta 34 sun bace bayan da jirgin ruwansu ya kife akan hanyarsu ta zuwa tsibirin Bakassi.

An samu ceto sojoji uku daga cikin 37 dake wannan jirgin ruwa mai suna “Le Mundemba”, wanda ya kife a jiya Lahadi da misalin karfe 6 na safe a kusa da gabar Debunsha.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta aikewa da manema labarai ta ce “har yanzu ba a tabbatar da musabbabin wannan hadari ba.”

Cikin gaggawa aka zuba ma’aikatan aikin ceto da bincike bayan da hanyar sadarwa ta katse tsakanin su da jirgin ruwan sojojin, har ya zuwa yau Litinin ana ci gaba da gudanar da binciken.

Kamaru dai ta karbi ikon yankin Bakassi mai albarkatun man fetur daga hannun Najeriya, shekaru uku da suka gabata a sakamakon wata yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ido wajen kullawa.

Mayar wa da kasar Kamaru wannan yanki ta kawo karshen shekara da shekarun da aka yi ana takaddama kan wake da mallakin wannan yanki.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG